Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : A wata sanarwa da t afitar da yammacin jiya, ta hanyar kafofin talabijin da radiyo na kasar, gwamnatin ta ce za’a rage tsawon tutoci domin juyayin wadanda suka rasu a harin.
Harin dai da wasu ‘yan bindiga kan Babura dauke da manyan makamai suka kai da yammacin ranar Litinin lokacin da suke aiki a gonakinsu ya yi sanadin mutuwar fararen hula 37 a kauyen Darey Dey, dake lardin Banibangou a yankin Tillabery.
A shekarun baya bayan nan yankin Tillabery yana fuskantar karuwar munanan hare-hare da ake kaddamarwa kan dakarun tsaron kasar da kuma fararen hula.
Daga farkon shekarar 2021, kimanin fararen hula 300 aka kashe a yankin, kamar yadda alkaluman hukumomi suka bayyana.
342/